15 Yuni 2025 - 00:29
Source: ABNA24
Daruruwan Makamai Masu Linzami Na IRGC Sun Afkawa Haifa A Isra'ila

Iran ta kai hari da makami mai linzami da dama a birnin Haifa ciki har da matatar mai na Haifa da ke arewacin yankunan da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti ta kasa da kasa ABNA ya bayar da rahoton cewa: majiyoyin yahudawa sun bayar da rahoton cewa, an kai wani hari da makami mai linzami kan birnin Haifa da ke arewacin yankunan da aka mamaye.

Rahoton ya ce, makamai masu linzami da Iran ta harba da dama sun afkawa birnin Haifa da ke arewacin Falasdinu da kewaye.

Bayan wannan harin makami mai linzami, gobara ta tashi a sassa daban-daban na birnin Haifa kuma hayaki ya tashi daga birnin zuwa sama.

Wasu kafafen yada labaran yahudawan sahyoniya sun kuma tabbatar da harin makami mai linzami kan matatar mai na Haifa.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha